Dalla-Dalla: Yadda Kula Da Jiragen Fadar Shugaban Kasa Ya Lashe N14.77bn Cikin Wata 11

Gwamnatin tarayya ta kashe kudin da yawansu ya kai Naira biliyan N14.77 domin gyara da kula da jiragen sama na fadar shugaban kasa a cikin watanni goma sha daya da suka gabata.

Jaridar Punch ta rawaito cewa an fitar da kudaden ne wata bayan wata har na tsawon watanni 11, farawa daga ranar 16 ga watan Yuli na shekarar 2023 zuwa ranar 25 ga watan Mayu na shekarar 2024 ta hanyar amfani da asusu na musamman da aka ware domin harkokin da suka shafi jiragen fadar shugaban kasa.

Wannan bayanai suna fitowa ne a daidai lokacin da majalisar wakilai ke cigaba da goyon bayan shirin siyawa shugaban kasa da mataimakinsa sabbin jirage guda biyu.

A cewar kwamitin tsaro na majalisar wakilai, jirgin sama kirar Boeing 737 da shugaban kasa ke amfani da shi tare da sauran jirage biyar da ke ayarin jiragen fadar shugaban kasa sun tsufa kuma basu da koshin lafiya.

Kwararru sun bayyana cewa siyen sabbin jiragen sama guda biyu na zamani zai lashe kudin da yawansu ya kai Dalar Amurka miliyan $623.4 kwatankwacin kudin Najeriya biliyan N918.7.

Gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kashe biliyan N62.47 wajen kula da jiragen fadar shugaban kasa a cikin shekara takwas na mulkinsa.

Binciken Punch ya nuna cewa shugaba Tinubu ya bayar da lamunin fitar da biliyan N14.77 a cikin shekara daya da hawansa mulki domin kula da jiragen.

KARANTA: Shettima, Tinubu da matarsa sun kashe N5.2bn a tafiye-tafiye, N12.5bn a kula da jirgi cikin wata uku

Wannan adadi bai hada da kudaden da aka kashe a kan jiragen ba yayin tafiye-tafiye na cikin gida da ketare da shugaban kasa da mataimakinsa suka yi.

Tinubu ya amince da kashe biliyan N1.52 na kula da jiragen a watan Yuli na shekarar 2023 tare da sake amincewa da kashe biliyan N3.1 a watan Agusta.

Sauran kudaden da aka fitar sun hada da biliyan N1.26 a watan Nuwamba na shekarar 2023. Biliyan N2.54 a watan Maris na shekarar 2024, biliyan N6.35 a watan Afrilu da kuma biliyan N1.27 a watan Mayu na 2024.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories