Abin Mamaki : Jihar Gombe Ta Ware N2.1bn Domin Yaƙar Cutar Korona

Duk da sanin cewar cutar korona a yanzu ta ɗauke ƙafa a Najeriya tun daga shekarar 2022,amma kuma kwatsam sai aka ji Gwamnatin Jihar Gombe ta ware Naira biliyan 2.1 don yaƙar cutar a cikin kasafin kudi na shekarar 2024, Wikkitimes ta labarto.

 A Binciken da WikkiTimes ta yi kan aikin kasafin kudi na Q1 2024 na Jihar ya nuna cewa Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Gombe ta rubuta cewar ta kashe kuɗaɗen yaƙar cutar  “Covid-19 ” wanda ya zarce kashi 211.3% na farkon kasafin kudin shekara a cikin watanni uku kacal na shekarar.

 Amma kuma an ji cewar Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta ba da rahoton cewa tun daga shekarar 2022, cutar COVID-19 aka yi nasarar daƙile barazanar ta ga lafiyar jama’a kamar yadda cutar ta haikewa mutane a 2020 da 2021.

Bayan rahoto ƙaewar cutar Korona da NCDC ta fitar ita kuma gwamnatin Gombe ta ce ta ware Naira biliyan 1 don cigaba da yakar cutar ta COVID-19 a cikin kasafin kudin 2024 wanda hakan ya ninka fiye da ninki biyu a cikin kwata na farko na 2024.

Sai dai kuma da aka tuntuɓi jin ta bakin gwamnatin jihar Gombe don bayar da bayanin yadda ta yi ashe-kashen maƙudan kudade a kan cutar ta COVID-19, nan take gwamnatin jihar ta musanta inda ta ke cewa tun farko ɗsn jaridar da ya wallafa labarin ya kirkiri adadin kuɗaɗen ne kafin daga baya ya koma ya kuma yi alkawarin yin gyara a raho.

 Babban daraktan hulda da manema labarai na gidan gwamnatin Gombe, Ismail Uba Misilli, yayin da yake mayar da martani kan binciken ya ce, “Ban san a ina dan jaridar nan ya samu wannan labari ba. Amma tabbas wanna ba shine abinda muka fitar a kasafin kuɗin mu na 2024 ba.”

 Ya bukaci cewa, “Da fatan za a tuntube su don sanin kan lamarin.”

Duk da dai har yanzu jaridar Wikkitimes bata samu wani cikakken amsa daga mahukunta lamarin ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories