‘Yar Atiku, El-Rufai Da Wasu ‘Yan Siyasar Arewa 6 Da Suka Mallaki Kadarori Na Fiye Da Tiriliyan A Dubai

Ƴan siyasar Najeriya sun ninka jarin da suke zubawa a bangaren gidaje na Dubai cikin shekaru hudu, a cewar wani bincike wata jarida mai wallafa rahotannin kasuwanci da bincike ta gudanar.

Binciken, wani bangare na aikin “Mabuɗin Dubai (Dubai Unlocked)” Binciken watanni shida na haɓakar Dubai da kasuwar mallakar kadarori cikin sirri wanda Cibiyar Bayar da Rahoton Laifuka da Cin Hanci da Rashawa (OCCRP) ke jagoranta tare da abokan aikin watsa labarai sama da 70, Economy Post ne kamfanin jarida daya tilo na Najeriya da ya shiga aikin, sun gano cewa: A shekarar 2020, an bankado kadarori 800 da kudinsu ya kai dala miliyan 400 (₦560bn) mallakin Ƴan siyasa Najeriya.

Ya zuwa shekarar 2024, adadin kadarorin ya karu zuwa 1,600, wanda darajarsu ta kai kusan dala biliyan daya (₦1.4 tiriliyan). – ‘Yan Najeriya su ne na biyu a kasashen ketare da ke sayan kadarori a Dubai, bayan Indiyawa.

Manyan jami’an tsaro, ma’aikatan gwamnati, da masu alaka da gwamnati da danginsu sun mallaki kashi 88% na kadarorin.

DUBA: Shettima, Tinubu da matarsa sun kashe N5.2bn a tafiye-tafiye, N12.5bn a kula da jirgi cikin wata uku

Kadarorin na nan a wurare masu daraja da alfarma, wadanda suka hada da: – Burj Khalifa – Palm Jumeirah – Marsa Dubai – Al Merkadh – Wadi Al Safa – Madinat Al Mataar – Nad Al Shiba First da sauransu.

Wasu daga cikin ‘yan Najeriya da suka mallaki kadarorin sun yi amfani da bayanan ƙarya ta hanyar sauya jinsi, tare da: – Wasu mazan da suka yi rijista da sunayen mata – wasu matan sun yi rijista a matsayin maza.

Rahoton ya fayyace cewa binciken ba laifi bane a kan mutanen da aka lissafa, saboda babu wata shaida da ta nuna cewa sun mallaki kadarorin ne da dukiyar jama’a.

Ga jerin sunayen su kamar haka :

ATIKU ABUBAKAR Wani fili mai daki uku da aka kiyasta kudinsa ya kai dala miliyan $1.23 a Palm Tower da ke Dubai.

YAR ATIKU MAI SHEKARU 23

Ta mallaki wani gida mai daki daya a Cibiyar Kasuwanci ta Biyu, wanda darajarsa ta kai $104,135. Ta kuma mallaki wani gida mai daki biyu a Hadaeq Sheikh Mohammed Bin Rashid wanda aka kiyasta a dala 289,305.75.

NASIR EL-RUFAI

Wani gida mai daki hudu wanda kudinsa ya kai $193,084 a Al Hebiah, an gano mallakin tsohon gwamnan Kaduna ne.

DUBA: N60, 000 ta yi yawa a matsayin mafi karancin albashi – Gwamnoni

YUSUF DATTI BABA-AHMED

Kaddarori takwas da aka kiyasta kudinsu ya kai dala miliyan $2.28 daga abokin takarar Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a zaben 2023. Kaddarorin suna a wurare masu kyau kamar Burj Khalifa, Al Yelaiss, Al Barsha South Fourth, da Town Square Safi 2.

ATTAHIRU BAFARAWA

Kadarori bakwai da kudinsu ya kai dalar Amurka miliyan $1.48, yayin da wata kadara ta gida da ke Palm Jumeirah kuma ta kai dala $750,112 mallakar matarsa ​​ce.

DUBA: Dalla-Dalla: Yadda Kula Da Jiragen Fadar Shugaban Kasa Ya Lashe N14.77bn Cikin Wata 11

AHMED MARKAFI

Wata kadara da ke Burj Khalifa wanda kudinsa ya kai $822,016 an gano mallakin tsohon gwamnan Kaduna ne.

AHMADU ALI

Wata kadara ce wacce ba a bayyana kimarta ba ta hannun tsohon shugaban jam’iyyar PDP ne, yayin da daya da aka kiyasta kudinta ya kai dala $422,887 ga diyarsa Khadijah Nneamaka Ali.

MAINA AJI LAWAN

An gano kadarori 11 ga tsohon gwamnan jihar Borno kuma Sanata.

AHMED ADAMU MUAZU
Matar tsohon shugaban jam’iyyar PDP, ta mallaki kadarar da ke Hadaeq Sheikh Mohammed Bin Rashid, wanda kudinta ya kai dala miliyan $1.16.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories