Yanzu – Yanzu : Gwamnatin Tarayya Ta Haramta Amfani Da Mazubin ‘Take Away’

Gwamnatin tarayya ta haramta amfani da robobin ‘Take Away’ a duk ma’aikatun gwamnati (MDAs).

Mazubin wanda ya kasance ana amfani da shi ne na lokaci ɗaya daga nan amfanin sa ya ƙare.

Da yake jawabi ga manema labarai a majalisar zartarwa ta tarayya (FEC), a yau Talata, karamin ministan muhalli, Iziaq Adekunle Salako, ya ce dokar hana amfani da mazubin an ƙaƙaba ta ne don tafiyar da  tsarin dq gwamnatin tarayya ta yi na ƙoƙarin sarrafa yawaitar bola.

 Ya ce, “Wannan yunƙurin yana nuna ƙudurinmu na magance barazanar sauyin yanayi,mutuwar ƙananan halittu da kuma magance ƙazanta”.

 Ministan ya bayyana tsananin gurbacewar da amfani da mazubin Take Away ya jawo a Najeriya, inda ya bayyana hakan a matsayin “babban al’amari da ya dame mu a kasarmu”.

 Ya kuma ce haramcin yin amfani da mazubin a ma’aikatu shiri ne na tunkarar yawaitar amfani da robobi a fadin ƙasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories