A Sirrance: FG Ta Shiga Cinikin Wani Jirgin Sama Na Alfarma, Ta Taya N150bn

Jaridar Premium Times ta wallafa wani rahoton bincike da bayyana cewa gwamnatin Najeriya tana shirin siyan wani jirgin alfarma “Airbus A330” da wani bankin kasar Jamus ya kwace daga hannun Balarabe dan sarauta da ke kasuwancin man fetur.

Balaraben Dan Kasuwar ya gaza biyan bankin bashin miliyon dalar Amurka da ya karba daga bankin yayin da zai sayi jirgin.

Duk da ma’aikan fadar shugaban kasa sun yi gum da bakinsu a kan batun cinikin jirgi, Premium Times ta ce ta samu bayanan da suka tabbatar da cewa tuni har gwamnati ta taya jirgin tare da mayar da hankali wajen yadda za a hada kudin da za a biya.

A cewar jaridar, ta gano cewa jirgin alfarmar da ake kokarin siya yana karkashin ikon wani bankin kasar Jamus da ba a bayyana sunansa ba, bankin ya mallaki jirgin ne bayan wani Balarabe Dan Kasuwa ya yi togaciya da shi a matsayin kadara mai daraja yayin da zai ranci kudi a bankin.

Majiyar Premium Times ta shaida mata cewa bankin ya fuskanci kalubale wajen siyar da jirgin saboda kudin da aka kashe masa domin kayatarwa da kayan kawa da alatu.

Yanzu haka jirgin yana karkashin kulawar wani kamfanin harkokin jiragen sama mai suna L & L International LLC da ke birnin Miami a jihar Florida ta kasar Amurka. Kamfanin L & L yana kokarin ganin cewa bankin na kasar Jamus ya siyar da jirgin ga gwamnatin Najeriya.

An yi kiyasin cewa darajar jirgin; mai injina da yawa, ta kai dalar Amurka $600. Gwamnatin Najeriya ta taya jirgin a kan kudin da da kadan suka haura dalar Amurka miliyan $100, kudin da yawansu ya kai Naira biliyan N150.

KARANTA: Gwamnatin Tarayya Ta Jingine Maganar Karin Albashi

Sai dai, majiyar Premium Times ta sanar da su cewa babu tabbas ko kamfanin L & L ya karbi tayin da gwamnatin tarayya ta yi.

Premium Times ta bayyana cewa wani kamfanin kasar Switherland; mai suna AMAC, da ke kwangilar kula da jiragen fadar shugaban kasa shine ya haskawa gwamnatin Najeriya batun jirgin tare da kwadaitawa gwamnati ta shiga cinikinsa.

Yanzu haka, kamfanin AMAC shine ya ke wakiltar Najeria wajen kulla cinikin jirgin da kamfanin L & L.

Majiyoyin Premium Times a fadar shugaban kasa sun sanar da ita cewa tuni fadar shugaban kasa ta mayar da hankali wajen ganiin yadda za ta tattara kudaden da za ta biya idan cinikin jrgin ya fada.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories