An Kama Mutum Biyu Dake Da Hannu A Satar Mahaifiyar Mawaƙi Rarara

Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu wajen yin garkuwa da mahaifiyar fitaccen Mawaƙi, Dauda Kahutu Rarara.

 Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, a wata sanarwa da ya fitar a yau Juma’a, ya ce yanzu haka waɗanda ake zargin suna ansa tambayoyi hukuma.

 “A yau Juma’a, 28 ga watan Yuni, 2024, da misalin karfe ɗaya, muka samu labari a hedikwatar ƴan sanda ta Danja cewa wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun mamaye gidan wata Hajiya Halima Adamu mai shekaru 75 a kauyen Kahutu, Danja.  LGA, jihar Katsina kuma suka yi garkuwa da ita.

 “Bayan samun rahoton, ba tare da bata lokaci ba DPO na Danja ya jagoranci tawagar jami’an tsaro zuwa wurin don fara gudanar da binciken kubutar da ita.

“A yayin gudanar da bincike, an kama mutane biyu da ake zargi a yanzu haka suna kan amsa tambayoyi ,Za sanar da duk wani abu dake faruwa yayin gudanar da bincike, “in ji sanarwar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories