Ku Daina Nuna Mugun Hali A Kan Karin Albashin Ma’aikata – NLC Ta Mayarwa Gwamnonin Martani

Kungiyar Kwadago ta Najeriya NLC ta yi Allah-wadai da kalaman da gwamnonin suka yi na cewa ya kamata jihohi su tantance tare da yanke mafi karancin albashi da zasu iya biya a yankunansu. 

“Ba zamu lamunci kama karya ko wasa da hankali ba daga gwamnonin jihohi wajen samar da mafi karancin albashi na kasa a Najeriya ba,” in ji kungiyar NLC a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Juma’a ta hannun jami’in yaɗa labarai da hulda da jama’a, Benson Upah.

Kungiyoyin kwadago, da gwamnati, da kuma kamfanoni masu zaman kansu sun shafe wattani suna tattaunawar neman sabon mafi karancin albashi.

Kwamitin haɗaka kan sabon mafi karancin albashi ya gabatar da N62,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi yayin da kungiyoyin kwadago suka dage a kan N265,000.

KARANTA: Gwamnatin Tarayya Ta Jingine Maganar Karin Albashi
Daga baya shugaba Bola Tinubu ya karbi rahoton kwamitin, inda ya yi alkawarin biyan abin da kasar za ta iya dauka. Har yanzu yana tuntubar masu ruwa da tsaki kafin daga bisani kuma ya aika da kudirin kafa sabon mafi karancin albashi ga majalisar dokokin kasa.

Kungiyar Gwamnonin jihohin kudancin Najeriya ta ce bai kamata mafi karancin albashi ya zama baiɗaya ba. Ya kamata jihohi su biya abin da za su iya, kar su takure kansu , in ji su.

“Majalisar ta tattauna kan batun mafi karancin albashin da ma’aikata ke nema, inda kuma baki daya sun amince da cewa mafi karancin albashi ya kasance daidai da tsadar rayuwa da kuma yadda za a iya biyan albashi, sannan a bar kowace Jiha ta tattauna kan mafi karancin albashin da ya kamaceta,” in ji gwamnonin a cikin sanarwar da suka fitar.

Sai dai, kungiyar NLC ta caccaki matakin da gwamnonin suka dauka, tana mai cewa “yana barazana ga jin dadin ma’aikatan Najeriya da tattalin arzikin kasa”.

KARANTA: Dalla-Dalla: Yadda Kula Da Jiragen Fadar Shugaban Kasa Ya Lashe N14.77bn Cikin Wata 11

“Kungiyar ta NLC ta caccaki gwamnoni da masu rike da mukaman siyasa a kan yadda suke nuna mugun hali kan batun mafi karancin albashi.

“Me ya sa ba za a yi kuka ba yayin da masu rike da mukaman siyasa a fadin kasar nan ke karbar albashi iri daya kamar yadda Hukumar Tattalin Arzikin Kasa da Kasa ta ta tsara? Tabbas duk wani mai kishin kasa ya dace ya damu da hakan.” kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Cire tallafin man fetur da kuma karyewar Naira wanda ya haifar da hauhawar farashin kayayyaki ya yi kamari, lamarin da ya ƙara dagula maganar sabon tsarin albashin ma’aikata.

KARANTA: Dalla-dalla: NLC ta fayyace dalilin kayyade N615,000 a matsayin mafi karancin albashi
A yayin tattaunawar, kungiyoyin kwadago da gwamnati sun yi muhawara mai tsawo amma har yanzu ba su cimma matsaya ba.

Ma’aikata sun fara yajin aikin gargadi, tare da rufe sassan tattalin arziki masu mahimmanci domin su samu biyan bukatunsu.

Kungiyoyin masu zaman kansu a karkashin kungiyar tuntubar ma’aikata ta Najeriya (NECA) sun yi gargadi kan biyan mafi karancin albashi da ya haura N62,000.

Hakan na zuwa ne bayan Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta yi jingine tattaunawa a kan wata takarda kan mafi karancin albashin ma’aikata domin sake tuntuba da neman karin shawarwari.

“Yanzu, idan ya wuce N62,000, kun ƙirƙiri matsaloli daban-daban. Na ɗaya, kun bada damar bijirewa “daya kenan. Domin idan ba zan iya biya ba, ba zan iya biya ba.

” Zaku kuma zaku haifar da matsala ga bangaren shari’a. Duk ma’aikatan da ba su gamsu ba, suna da ‘yanci, kamar yadda doka ta tanada, su garzaya kotun masana’antu ta kasa,” a cewar Darakta-Janar na NECA, Adewale Oyerinde.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories