Ƴan Bindigan Sun Buƙaci N900M Kudin Fansan Mahaifiyar Rarara

Ƴan bindigan da suka yi awon gaba da Hajiya Hauwa’u Adamu mahaifiyar fitaccen mawaƙin Hausa, Dauda Adamu wanda aka fi sani da Rarara, sun buƙaci danginta da su biya kuɗin fansa N900m.

 Wata majiya da ke kusa da iyalan Rarara wanda ta nemi a sakaya sunanta ta bayyana wa Daily Trust cewa da farko waɗanda suka sace ce hajiar sun kira a waya inda suka bukaci N1bn da farko.

Majiyar ta cigaba da cewa :“Sun kira mu da  wayar ɗaya daga cikin matan da suka tarar a daƙi lokacin da suka zo ɗaukar Hajiya.Inda Suka buƙaci N1bn amma bayan takaitacciyar tattaunawa da wani dan uwa sai suka rage kudin zuwa N900m.

 “Da farko sun bukaci yin yarjejeniya da shi Rarara saboda rashin lafiyar data kwantar da shi sakamakon sace mahaifiyarsa, Sai suka amince su kulla yarjejeniya da wani daga cikin ƴan uwa  Sun tabbatarwa yan uwa cewa Hajiya tana cikin koshin lafiya kuma da zarar an biya kudin za a sako ta.Bayan wannan tattaunawa zuwa yanzu dai ƴan bindiga basu sake kira ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories