Sanadiyyar Ƙwallo Wani Matashi Ya Rasa Ransa A Jami’ar Tarayya Da Ke Gombe

Musun ƙwallon ƙafa da ya ɓalle tsakanin wasu matasa a Jami’ar Tarayya Kashere da ke Jihar Gombe, ya yi sanadin mutuwar Abdussamad Musa, ɗalibi ɗan aji biyu a fannin ilimin laifuka da tsaro.

 Lamarin dai ya faru ne a ɗakin kwanan ɗalibai da ke wajen makarantar, inda wasu dalibai suka caka masa wuka a wuya, sakamakon wata zazzafar muhawara kan ƙwallon ƙafa da ya shiga tsakanin su.

KU KARANTA :

 A cewar shaidun gani da ido, rikicin ya faro ne tun da sanyin safiya, sai dai abun ya ta’azzara ne bayan da gungun daliban suka sake dawowa a ƙaro na biyu don cigaba da tafka muhawaran wanda hakan ya kai ga rasa rai.

 Wani abokin marigayin mai suna Aliyu Usman, na sashen kimiyyar siyasa ya shaida wa WikkiTimes cewa an ”fara cece-ku-ce ne a kan kwallon aka gama aka watse daga baya kuma sai suka sake dawowa wanda hakan ya jawo hatsaniya  har takai ga Jama’a sun fara fitowa daga gidajensu, bayan fitowarsu, sai aka yi taho-mu-gama, inda aka caka wa Abdusamad wuƙa a wuya ”

Wakilan Dalibai ta Jami’ar (SRC) ta yi Allah wadai da faruwar lamarin, ta kuma sha alwashin yin adalci, tare da haɗa kai da hukumomin tsaro domin tabbatar da hukunta wadanda suka aikata wannan aika – aika.

Babban jami’in tsaro na jami’ar, Mukhtar Zailani, ya tabbatar da cewa yanzu haka an kama waɗanda ake zargi su 13 ciki hadda shugaban tawagar Iliya Mshelia.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories