Najeriya Ta Biya Kamfanin Jiragen Saman Turai Bashin Da Take Binta

Gwamnatin tarayya ta hoɓɓasa ta biya  bashin dala miliyan 850 da kamfanonin jiragen sama na Turai ke binta kamar yadda kungiyar Tarayyar Turai EU ta bayyana.

 Jakadiyar Tarayyar Turai a Najeriya da kungiyar ECOWAS, Samuela Isopi,ita ce ta bayyana hakan a wajen taron kasuwanci da ya gudana tsakanin Najeriya da EU karo na 9 a Abuja.

KU KARANTA :

Taron mai taken ‘Zuba hannun jari don amfanin gaba mai dorewa’ wanda ya samu halartar babban darakta a kungiyar ta EU, Myriam Ferran, ministan kasafin kuɗi da tsare-tsare na ƙasa, Atiku Bagudu, da kuma babban sakatare a ma’aikatar masana’antu, Ciniki, da Zuba Jari, Ambasada Nura Rimi.

 A wajen taron, EU da Eurocham Nigeria (The European Business Chamber) sun rattaɓa hannu kan yarjejeniyar bayar da tallafi na Yuro 300,000 don tallafa wa ci gaban haɗakar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories