NDLEA : Za A Fara Yiwa Ma’aurata Gwajin Ƙwaya A Kano

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA a Kano ta yi kira ga majalisar dokokin jihar da ta ɗabbaka dokar fara yiwa ma’aurata gwajin ƙwaya kafin aure domin rage yawan shaye-shayen miyagun ƙwayoyi a jihar.

 Kwamandan NDLEA a Kano, Abubakar Idris-Ahmad shi ne ya bayyana haka ga kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a yau Alhamis.

“Hukumar ta bullo da shirin gwajin ƙwayoyin ne wanda ake sa ran zai zama al’ada domin ganin an yaki yammaci da miyagun ƙwayoyi ga kowane dan Najeriya,” in ji shi.

KU KARANTA :

 Idris-Ahmad ya ce gwajin ƙwayan zai zama wani makami ne na rigakafin shan muggan kwayoyi da kuma saurin gano cikin ma’auratan waye ke sha domin taimaka musu wajen ganin an magance wannan matsalar.

Ya ce dokar da aka tsara na gwajin ya zama dole a ɗabbaƙata domin magance yawaitar tabarbarewar aure da kuma rage shaye-shayen miyagun kwayoyi a tsakanin ma’aurata a jihar.

 “Bincike ya nuna cewa cikin mata da miji ɗaya ne ke koya wa ɗan uwansa ta’ammali da ƙwayoyin bayan sun yi aure har ma sun hayayyafa wanda hakan yana matuƙar wahala wajen magancewa.”

 Kwamandan Ya yi kira ga majalisar dokokin jihar Kano da ta kafa dokar da za ta halasta yin gwajin ƙwaya kafin aure.

 Sannan Kwamandan ya yi kira ga mata da matasa da ma sauran jama’a da su guji shaye-shayen miyagun kwayoyi sannan kuma su bada hadijn kai domin ciyar da jihar gaba da ma ƙasa baki ɗaya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories