Wasu da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne sun tarwatsa Tiransfomar wutar lantarki mai karfin 330KVA a jihar Yobe, lamarin da ya yi sanadin rashin wuta a jihar.
Mai baiwa Gwamna shawara Janar Ɗahiru Abdulsalam (mai ritaya), shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Damaturu.
![](https://wikkitimes.com/hausa/wp-content/uploads/2023/12/IMG_7761.webp)
Ya ce ƴan ta’addan sun tarwatsa Tiransfomar ne ta hanyar fashewar bama-bamai, a yankin Kasesa a daren ranar Alhamis.
Mai Baiwa Gwamna shawara na musamman ya ce lalacewar Tiransfomar ta yi sanadiyyar rashin wuta a jihar.
Ya ce gwamnatin jihar tare da hadin gwiwar sashin 2, Operation Haɗin Kai, da kamfanin rarraba wutar lantarki na Yola, YEDC, suna kokarin ganin an shawo matsalar rashin wutan.
NAN