Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya amince da nadin sabbin manyan sakatarori guda takwas a matakin gwamnatin tarayya domin cike gibin da ake da shi na rashin wakilci daga wasu bangarori na Najeriya.
An zabi sabbin manyan sakatarorin ne bayan ofishin shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya ya tantance su. Wadanda aka nada sun hada da;
1) Dr. Emanso Umobong Okop daga jihar Akwa-Ibom
(2) Obi Emeka Vitalis daga jihar Anambra
(3) Mahmood Fatima Sugra Tabi’a daga jihar Bauchi
(4) Danjuma Mohammed Sanusi daga jihar Jigawa
(5) Olusanya Olubunmi daga jihar Ondo
(6) Dr. Keshinro Maryam Ismaila – Zamfara
DUBA WANNAN: Abinda Atiku Da Buhari Suka Tattauna Yayin Ganawarsu A Daura
(7) Akujobi Chinyere Ijeoma daga yankin Kudu maso Arewa
(8) Isokpunwu Christopher Osaruwanmwen daga yankin Kudu maso Kudu
A wata sanarwa da mai taimakawa shugaba Tinubu a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale, ya fitar ranar Juma’a, 28 ga Watan Yuni, ya ce sabbin sakatarorin zasu yi amfani da kwarewarsu ta aiki wajen taimakon gwamnati da kawo cigaba ga kasa da ‘yan kasa.