Manyan illolin Sanya Matsatstsen Ɗan Kamfai Ga Maza

Da yake maza da yawa suna sa matsatstsen ɗan kamfai ne domin ƙara suturta al’aura. Kuma hanya ce ta tsare al’aurar daga bayyana musamman bayan sa manyan tufafi kamar riga ko wando.

Sai dai, masana sun ce sa matsatstsen ɗan kamfai na da illa ga lafiya.Yadda lamarin yake shi ne, a cikin ƴaƴan maraina ake samarwa tare da adana maniyyi wanda ya ƙunshi ƴaƴan rai, wato “sperm cells” a turance.

Ƴaƴan rai sune ƙwaiƙwayen haihuwa na ɗa namiji.Daga cikin hikimar Allah na saukar da jakar ƴaƴan maraina ƙasa daga jiki akwai samar da ɗumi ƙasa da ɗumin jiki. Wato ƴaƴan maraina suna buƙatar muhalli mai sanyi fiye da jiki domin samar da lafiyayyun ƴaƴan rai.

Saboda haka, saukar da jakar ƴaƴan maraina ƙasa da jiki yana samar da raguwar ɗumi da maki 4 — 6 a ma’unin salsiyos ƙasa da ɗumin jiki, wanda shi ne kyakkyawan yanayin da ƴaƴan maraina za su iya samarwa tare da adana lafiyayyun ƴaƴan rai.

Don haka, sanya matsatstsen ɗan kamfai zai ɗaga jakar ƴaƴan maraina tare da ɗanfare ta ko takure ta da jiki. Hakan kuma zai sa yanayin ɗumin ƴaƴan maraina ya ƙaru kuma ya saje da na jiki.

Bincike ya nuna cewa, maza da suke sa matsatstsen ɗan kamfai tsawon rana suna da ƙarancin adadin ƴaƴan rai idan aka kwatanta su da mazan da ba sa sa matsatstsen ɗan kamfai.

Bugu da ƙari, sa matsatstsen ɗan kamfai na taƙaita ko rage gudanarwa jini a al’aura, wanda hakan na iya haifar da matsaloli ga lafiyar al’aura.

Har wa yau, ta ɓangaren tsafta kuwa, sa matsatstsen ɗan kamfai na haifar da gumi tare da riƙe danshi ga al’aura da kewaye.

Hakan kuwa na iya janyo cutukan fata a al’aura da kewaye.Zaɓi ɗan kamfai mai yalwa wanda ba zai takura al’aura ba.

Daga shafin Physiotherapy Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories