Daga cikin matsalolin da yara, musamman ‘yan ƙasa da shekara biyu ke fuskanta yayin raino akwai matsalar nan da ake kira da ‘Shaken Baby Syndrome’ a turance. Wannan matsala ce da yara ke fuskanta yayin jijjigawa a ƙoƙarin lallashin su yayin da suke kuka ko kuma yayin yi musu wasa.
Yara sun fi fuskantar wannan ƙalubale ne musamman yayin da suke hannun masu raino ko kuma iyayensu maza.Jijjiga yara na da gagarumar illa ga ƙwaƙwalwa, wani lokacin ma na iya sanadiya mutuwar yaro.Kamar yadda aka sani, wuya ne ke ɗauke da kai, kuma tsaiwa ko daidaituwar kai ya dogara ne ga ƙwarin tsokokin wuya.
Yadda Malamin Tsubbu Hassan Patigi Ke Azabtar Da Masu Jinya, Yi Wa Mutane Tsirara Tare Da Amshe Musu Kuɗaɗe
Sama da shekaru, Malam Hassan Patigi, daga yankin Patigi a jihar Kwara ya kasance na rangadi a garuruwa da ƙauyuka da dama a Najeriya da manufarsa na yunƙurin warkar da marasa lafiya da cetosu mutane daga ƙaƙaniƙayin damuwowi da rashin lafiyar da ya musu katutu. Sai dai, a ƙoƙarinsa na kai wa ga cimma hakan,…
Shugaban Ƙasar Iran Raisi Ya Rasu A Wani Hatsarin Jirgi
Wani jirgin sama mai saukar ungulu ɗauke da wasu daga cikin manyan kasar Iran ciki har da shugaban kasar Ebrahim Raisi ya Yi hatsari a jiya lahadi. Hatsarin wanda rahotanni suka tabbatar da cewa ya yi sanadiyyar mutuwar duka mutanen da ke cikin jirgin . Jirgin mai saukar ungulu wanda ke kan hanyarsa daga Tehran zuwa Tabriz, ya faaɗo ne a jiya lahadi Daga…
Tsokokin wuyan yara ‘yan ƙasa da shekara biyu kuwa ba su gama yin ƙwarin da zai iya riƙe kan sosai ba, musamman yayin jijjiga su. Saboda haka, jijjiga su na iya yin lahani ga ƙwaƙwalwarsu, da kuma janyo mummunan rauni ga wuya wanda na iya shafar laka.
Daga cikin matsalolin da ke biyo bayan jijjiga yaro akwai:
1. Ɓallewar jijiyoyin jini a cikin kai.
2. Bugun ƙwaƙwalwa, idan ƙwaƙwalwa ta bugu da ƙoƙon kai daga ciki.
3. Takura ƙwaƙwalwa; yayin da jini ya taru a gefe ko kewayen ƙwaƙwalwa zai takura ko matse ƙwaƙwalwar ne.
4. Katsewar iskar oksijin zuwa ƙwaƙwalwa, saboda numfashinsu na ɗaukewa yayin jijjiga su.
5. Lahani /rauni ga laka.
6. Karayar ƙoƙon kai idan aka buga kan yaro da bango, kujera, daɓe da suransu yayin jijjiga su, hakan kuma zai iya janyo karaya a ƙoƙon kai.
Akwai buƙatar iyaye da su sake lura saboda wannan matsala ba a gane ta afku a zahiri saboda ƙwaƙwalwa take shafa.
Sai dai, yaron da ya fuskanci jijjigawa sosai na iya nuna wasu alamu da zarar an jijjiga shi zuwa awanni shida.Alamun sun haɗa da:
1. Fita daga hayyaci
2. Amai3. Suma
4. Ƙin karɓar abinci/abinsha
5. Kakkafewar jiki ko jijjiga irin ta masu farfaɗiya
6. Numfashi ƙasa-ƙasa ko kuma riƙicewar salon numfashi.
Ana sa ran warkewar yaron da ya samu wannan matsala ne gwargwadon girman raunin da ya afku a ƙwaƙwalwar.
Matsalolin da ke biyo baya sun haɗa da:
1. Shanyewar ƙwaƙwalwa.
2. Shanyewar ɓarin jiki ko ɓangarorin biyun duka.
3. Dakushewar kaifin ƙwaƙwalwa.
4. Farfaɗiya, da sauransu.
Daga ƙarshe, ya kamata iyaye su sake sanya ido domin magance matsalar jijjiga yara musamman yayin bayar da su raino.
A garzaya asibiti da yaro da zarar ya nuna alamun da aka ambata bayan an jijjiga shi ko kuma an buga kansa da wani abu.
Daga shafin Physiotherapy Hausa