Badakalar daukan aiki: Kotu ta daure Kwamandan NSCDC na shekara biyar

Wata kotu a jihar Katsina ta daure kwamandan hukumar tsaro ta ‘Civil Defense’ biyo bayan gurfanar da shi da hukumar ICPC mai yaki da cin hanci da rashawa tayi.

ICPC ta gurfanar da kwamandan mai suna Christopher Oluchukwu bisa tuhumarsa da hannu dumu-dumu a badakalar daukan aiki a hukumar NSCDC.

A karar da ICPC ta shigar, ta zargi Oluchukwu da karbar kudi N200,000, da N300,000 da N400,000 daga wurin wasu mutane uku da ‘ya’yansu ke neman aiki a hukumar NSCDC.

Iyayen masu neman aikin sun shigar da korafinsu a gaban hukumar ICPC bayan Oluchukwu ya gaza samarwa ‘ya’yansu aiki sannan kuma ya gaza dawo musu da kudinsu.

Lauyan hukumar ICPC, Ibrahim Garba, ya sanar da kotu cewa laifin da Oluchukwu ya sabawa sashe na 8, da na 10 da na 19 na kundin yaki da cin hanci da rashawa na shekarar 2000.

A wani labarin da WikkiTimes Hausa ta wallafa, hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, tare da ‘yarsa, Fatima, da kuma surukinsa a gaban kotu.

KARANTA: Bashin $350m: Majalisar Jihar Kaduna ta fara binciken El-Rufai

Babbar kotun ta Abuja ta amince da bayar da belin Sirika tare da sauran wadanda aka gurfanar tare da shi akan N100m kowanne mutum tare da mutum biyu da zasu tsayawa kowa.

A cewar kotun, dole wadanda zasu tsaya domin karbar beli su kasance ‘yan kasa nagari kuma masu kadara a Abuja.

Alkalin kotun, Jastis Sylvanus Oriji, ya bada umarnin a tsare wadanda aka gurfanar a gidan yari idan basu cika sharadin beli ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories