Sojoji Sun Ceto Mutane 6 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kebbi

Dakarun sojojin Najeriya da haɗin gwiwar ƴan banga a ranar juma’ar da ta gabata sun yi nasarar ceto wasu mutane shida da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a wani daji da ke ƙaramar hukumar Shanga a jihar Kebbi .

 Mai bai wa Gwamna shawara na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Malam Yahaya Sarki, shi ne ya bayyana haka a Birnin Kebbi a jiya Asabar inda ya ce an yi nasarar kubutar da duka mazan da aka yi garkuwa da su cikin koshin lafiya, kuma an dawo da su ga iyalansu.

 “Dakarun Bataliya ta ɗaya, Barrack Dukku, Birnin Kebbi, tare da ƴan banga sun kai farmaki tsaunin Kogon Damisa da ke kusa da Saminaka a karamar hukumar Shanga, garin da ke kan iyaka tsakanin Kebbi da Neja a ranar Juma’a.

 “Rundunar ta yi nasarar fatattaki yan bindiga da dama tare da ceto mutane shida da aka yi garkuwa da su.

“Dama an sanar da rahoton ɓacewar su waɗanda aka yi garkuwa da su da daɗewa in ji mai baiwa Gwamna shawarar.

 Sarkin yankin ya yabawa ƙwazon sojojin tare da jaddada kudirin gwamnati na tallafawa hukumomin tsaro a jihar

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories