Ƴan Sanda Sun Damƙe Wani Mutum Da Laifin Lalata Da Wani Yaro A Bauchi

Rundunar ƴan sanda ta cafke wani mutum mai shekaru 40 da laifin yin lalata da wani Ɗan makwabcinsa mai shekara biyar . Iyayen yaron su ne suka yi ƙoƙarin kai rahoton faruwar lamarin a garin Azare, hedikwatar karamar hukumar Katagum ta jihar Bauchi.

 Malam Nuhu Abubakar Azare, mahaifin yaron wanda aka sakaya sunansa ya shaida wa WikkiTimes cewa an dade ana cin zarafin yaronsa amma danginsa babu wanda ya nuna halin ko in kula.

 “Na aminta da shi sosai kasancewar sa maƙwabcina ban taba zaton zai yiwa iyalina haka ba. Ƴaƴa na da nashi ana zaman ɗaɗi,” cewar malam Nuhu.

 Ya ƙara da cewa maƙwabcin na sa a kwanakin baya ya taɓa haurowa ta katangar gidan sa don cin zarafin yaron wani lokaci da suka tafi wani kauye ta’aziyya da matar sa .

”Ko da zamu tafi ta’azziya mun umurci yaran mu da su rufe ƙofa su zauna a gida kar suje ko ina”.

”Ɗana ya sanar min cewa makwabcinmu ya hauro gidan mu wanda haka ya bata min rai matuka.”

 Safara’u Muhammad, mahaifiyar Yaron ta bayyana cewa bayan da ta ga wasu sauye-sauyen ɗabi’u masu ban al’ajabi a tare da Ɗanta, sai ta tuhumi yaron inda shi kuma ya bayyana mata Gaskiya.

 “Lokacin da na yi zargin wani abu sai na tsareshi shine ya ke gaya min cewa maƙwabcinmu da ɗansa suna saka yatsa da wani baƙin abu a dduburata.Ya Kuma ce zai buge ni ya kashe ni idan na gaya wa kowa,” mahaifiyar ta shaida wa WikkiTimes.

Malam Nuhu ya ce bayan ya kai rahoton lamarin ga ofishin ƴan sanda da ke Azare, Nan take aka umarci a duba lafiyar yaron wanda hakan ya tabbatar da tabbas an taɓa shi yaron.

 “A yanzu haka da nake magana da ku, yakan ce min in goge masa duburar sa.  A yanzu abun ƙara gaba kawai yake yi. INa kira ga hukumomi da su tabbatar da gudanar da bincike kan lamarin kuma a hukunta wanda ya aikata laifin,” inji mahaifiyar yaron a wata hira da Wikktimes ta yi da ita ta wayar tarho.

Sai dai kuma Kakakin rrundunar ƴan sandan Bauchi, Sufeto Ahmed Wakil, ya katse kiran wayar da aka yi masa da aka tambaye shi game da lamarin.

Ya ƙi amsa kiran da aka yi masa ta wayar sa kuma ya ƙi amsa sakon WhatsApp da aka tura masa duk da ya karanta.

 Luwadi babban laifi ne a kotun shari’ar jihar Bauchi .

 A shekarar 2022 ne wata kotun shari’a a jihar Bauchi ta yanke wa wasu mutane uku hukuncin kisa ta hanyar jefe su bayan samun su da laifin yin lalata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories