An Wayi Gari Da Mutuwar Wasu Makiyaya A Garin Abuja

An sami rahoton kisan wasu makiyaya biyu a wani harin ramuwar gayya da aka kai a wani rigar Fulani da ke ƙauyen Kpache masarautar Yaba a ƙaramar hukumar Abaji a babban birnin tarayya Abuja.

City & Crime ta ruwaito cewa a ranar Asabar ɗin data gabata ne hatsaniya ta ɓarke tsakanin wasu ƴan banga da makiyaya a kasuwar Yaba , lamarin da ya yi sanadiyar kashe wani ɗan banga, wanda ya fito daga ƙabilar Bassa .

Wani mazaunin garin Yaba, Saidu Shuaibu, wanda ya tabbatar da kisan makiyaya biyu ga wakilin Daily Trust a ranar Laraba, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 11 na dare.

Ya ce maharan sun kai hari sansanin makiyayan inda suka yi nasarar harbe mutum biyu wanda hakan ya haifar da tashin hankali a yankin.

An yi ƙoƙarin jin ta bakin Kakakin rundunar ‘yan sandan Abuja, SP Adeh Josephine,abun ya ci tura sakamakon rashin maida martani ga sakon kar ta kwana da aka tura .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories