Ƴan bindiga sun yi awon gaba da shugaban ƙaramar hukumar Akwanga da ke jihar Nasarawa

Rahotanni daga jihar Nasarawa da ke tsakiyar Najeriya sun bayyana cewa wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da shugaban ƙaramar hukumar Akwanga, Safiyanu Isa Andaha.

Jami’an ƴan sanda a jihar sun bayyana cewa, an sace jami’in ne ranar Litinin da daddare a ƙauyen Ningo da ke kan titin Andaha – Akwanga, tare da wani dan asalin yankin.

A cewar jami’in hulda da jama’a na ƴan sandan, Ramhan Nansel, jami’an tsaro da suka haɗa da na ƴan sanda sun fara bin diddigin waɗanda suka yi garkuwa da su cikin gaggawa domin ganin an sako mutanen.

Jihar Nasarawa dai kamar Zamfara na ɗaya daga cikin jihohi a Najeriya da ake fama da ta’addanci da ƴan bindiga ke kai farmaki kauyuka suna kashe mutane da kuma sace su.

Najeriya dai na fuskantar dimbin kalubalen tsaro da suka hada da rikicin jihadi na tsawon shekaru 14 a yankin arewa maso gabas wanda ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 40,000 tare da tilasta wasu fiye da miliyan biyu barin gidajensu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories