Yadda Ɗan Daba ya Hallaka Limami Saboda Ya Hana Shi Shan Tabar Wiwi a Kano

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya reshen Jihar Kano ta ce ta kama wani dan daba kan zargin kashe wani limami saboda ya hana shi shan wiwi a Kano.

A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a ranar Laraba, dan daban mai suna Yusuf Haruna dan shekara 18 wanda aka fi sani da Lagwatsani ya caka wa malamin wuka a bayansa yana tsaka da alwala.

“A ranar 31 ga watan Disambar 2023 da misalin bakwai da rabi na dare, an samu rahoto daga wani Musa Yunusa da ke unguwar Jakara Kano kan cewa da misalin karfe bakwai na safe wani Yusuf Haruna ya caka wa Malam Sani Mohammed Shuaibu wuka a baya yana tsaka da alwala.

“Ya caka masa wukar sakamakon ya gargade shi kan ya daina zukar tabar wiwi a kusa da masallaci,” in ji sanarwar.

Rundunar ‘yan sandan ta ce sakamakon haka ne malamin ya samu rauni wanda aka garzaya da shi asibitin Murtala inda likitoci suka tabbatar da ya rasu.

Hukumar ‘yan sandan ta Kano ta tabbatar da cewa tana ci gaba da bincike kan wannan lamari kuma da zarar ta kammala za ta gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu.

Ko a cikin watan Disambar da ya gabata sai da aka caka wa wani matashi mai suna Nafi’u wuka a Kano, wanda hakan ya yi sanadin mutuwarsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories