Fiye Da Rabin Al’ummar Duniya Za Su Yi Fama Da Teɓa Nan Da Shekarar 2035

Hukumar nazari kan ƙiba fiye da kima ta duniya ta yi gargaɗin cewa sama da rabin al’ummar duniya za su yi fama da teɓa nan da shekara ta 2023, matuƙar ba a ɗauki matakin da ya dace ba.

Rahoton hukumar ya ce sama da mutum biliyan huɗu ne za su yi fama da matsalar ta ƙiba fiye da kima.

An yi ƙiyasin cewa za a iya kashe kuɗi sama da dalar Amurka tiriliyan huɗu wajen yaƙi da matsalar a ƙasashen masu ƙarami da kuma masu matsakaicin ƙarfi a nahiyar Afirka da kuma Asiya nan da shekarar ta 2035.

Shugabar hukumar, Farfesa Louise Burr ta bayyana rahoton a matsayin gargaɗi ga ƙasashen duniya kan su ɗauki mataki game da matsalar nan take, idan ba haka ba lamarin zai yi gagarumar illa a nan gaba.

Rahoton ya nuna damuwa kan cewa matsalar za ta fi yin illa ne ga yara da matasa, waɗanda ake sa ran yawan masu fama da matsalar a cikinsu zai nunka a shekaru masu zuwa.

Farfesa Louise ta ce akwai buƙatar hukumomi da ƙungiyoyi da kuma gwamnatocin ƙasashen duniya su yi mai yiwuwa wajen daƙile lamarin domin kauce wa illar da za ta yi wa lafiyar al’ummar da ke tasowa.

Rahoton ya kuma bayyana tasirin teɓa a ƙasashe masu ƙaramin ƙarfi, inda ya bayyana cewa ƙasa tara cikin 10 da ake sa ran za su yi fama da matsalar teɓa matsakaita ko kuma marasa ƙarfi ne a nahiyar Afirka da Asiya.

Ɗaya daga cikin dalilan da za su ta’azzara matsalar shi ne sauyi da za a samu a wajen wadatar cimaka mai gina jiki da kuma rashin motsa jiki.

Wasu dalilai da za su iza wutar matsalar su ne rashin ingantaccen tsarin kiwon lafiya a ƙasashen, da rashin ilimi kan batun da kuma iyaye waɗanda ba su da wayewa kan matsalar.

Rahoton ya ce ƙasashe marasa ƙarfi sun ce ba su shirya yadda ya kamata ba wajen shawo kan matsalar da illolinta.

Rahoton ya ƙara da cewa matsalar teɓa za ta kuma yi illa ga tattalin arziƙin duniya.

Ana sa ran miƙa rahoton ga Majalisar Dinkin Duniya.

Matsalar teɓa ko ƙiba fiye da kima na nufin wani yanayi da mutum ke samun kitse a jikinsa fiye da yadda yake buƙata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories