Dalilai 10 Da Suka Sa Gwamnatin Tinubu Ya Fi Na Buhari

 Reno Omokiri Mai Fashin baƙi a harkar siyasa ya bayyana wasu lamurra da su ka sa Gwamnatin Tinubu ta Fi tsohuwar gwamnatin Buhari.Reno ya bayyana manyan Dalilai har goma sha biyu wanda suka ja layin bambanci tsakanin gwamnatocin biyu.

 Na farko Najeriya ta fuskanci koma bayan tattalin arziki shekaru ashirin da suka wuce, abin mamaki watanni uku bayan hawan Buhari mulki sai aka sake samun irin haka a shekarar 2020. Amma, a cewar Standard and Poor’s, babbar hukumar tantancewa ta duniya, da Fitch, da Moody’s, tattalin arzikin Najeriya ya samu ci gaba a cikin watanni shidan farko na mulkin Tinubu.

 Na Biyu A zamanin Buhari, NGX ta yi asara mai yawa. Amma a ƙaƙashin Tinubu, NGX ta sami riba mai yawa. A ranar 5 ga watan Janairu, 2004, NGX ta hauhawa da maki 80,000 a karon farko, a cewar Ƙungiyar Kasuwanci ta London.

Sannan A zamanin Buhari an samu canji Naira da yawa, kuma babban bankin Najeriya yana kashe dala biliyan 1.5 duk wata don kare Naira. A karkashin Mulkin Tinubu kuwa Naira ta yi daraja, kuma an daidaita farashin canji a hukumance.

 Abu na Huɗu : A zamanin Buhari an kare ministocin da ake zargi da cin hanci da rashawa amma ƙarkashin Tinubu kuwa , an dakatar da su ana bincike.

 Abu na Biyar Buhari ya zurawa hukumar NSIP ido ta zama hanyar cin hanci da rashawa.  Amma Tinubu ya dakatar da hakan.

Abu na Shida A mulkin Buhari ƴan Najeriya ba su iya samun fasfo, saboda hukumar shige da fice ta Najeriya ta koka da ƙarancin faifan. Amma A karkashin Tinubu, ƴan Najeriya yanzu suna samun fasfo dinsu a cikin mako guda ko kasa da haka a lokuta da dama.

 Abu na Bakwai: Gwamnatin Buhari ta haramta cryptocurrency, tare da rufe ƴan Najeriya daga cikin masana’antar dala tiriliyan 1.8. amma sai Gwamnatin Tinubu ta dage wannan haramcin, kuma dubban daruruwan matasa Najeriya masu basira yanzu suna samun kuɗi da crypto, maimakon shiga yahoo.

 Abu na Takwas: Buhari ya ba da umarnin rufe iyakokin ƙasa, wanda hakan ya yi illa ga masana’antunmu, domin kayayyakin da aka samar daga Najeriya ba sa iya isa har makwabtanmu. Rufe kan iyakokin ne ya janyo hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya wanda ya ƙaru da lambobi biyu, daga mai lamba daya da Buhari ya gada daga Jonathan.  Sai dai Gwamnatin Tinubu na neman hanyoyin magance wannan batu.

Abu na Tara A zamanin Buhari, karancin man fetur ya kasance, ruwan dare. A karkashin Tinubu, kuwa an samar da man fetur sosai, inda Shugaban kasa ya cika alkawarin da ya dauka kan matatar mai ta Fatakwal, kuma ya yi aiki a matsayin hanyar da za ta sa matatar man Dangote ta fara aiki, kamar yadda Dangote da kansa ya shaida.

 Abu naGoma A ranar 12 ga Disamba, 2016, sojoji ƙarkashin Buhari sun mamaye Zariya, sun kashe maza da mata da kananan yara da jarirai 248 na kungiyar ƴan Shi’a. Babu wani mutum guda da aka kama, ko aka yi masa shari’a, ko kuma aka yanke masa hukunci kan wannan kisan kiyashin.  A karkashin Tinubu, an kama wasu sojoji da suka azabtar da wani farar hula a Rivers kuma suna fuskantar shari’a.

 Abu na Goma sha daya A zamanin Buhari, wani dan sanda ya ƙi bin doka da oda da tsarin mulki na Gwamnan Legas lokacin da ya umarce shi da ya sa mutanensa su bar yankin Magodo, inda suka yi wa kawanya.  Ba a yi masa komai ba.  A karkashin Tinubu, wannan Gwamnan ya damke wani sojan da ke tukin ganganci a kan hanya, da wsni soja ya yi faifan bidiyo yana zagi an kama shi.

 A lokacin mulkin Buhari wasu ‘yan bindiga sun mamaye hanyar Abuja zuwa Kaduna, sun kai hari a filin jirgin saman Kaduna dauke da makami a babura, inda suka kutsa cikin NDA suka kashe sojoji, tare da tayar da bam a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.  A yau ƴan Najeriya na iya tafiya ta hanyar mota da jirgin kasa da ta jirgin sama tsakanin Abuja da Kaduna cikin kwanciyar hankali.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories