Jami’an DSS Sun Kama Bello Bodejo Kan Kafa Rundunar Sa-kai Ta Fulani Zalla

Jami’an hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta kama shugaban ƙungiyar Miyetti Allah Kautal Hore, Bello Bodejo, kan kafa rundunar sa-kai ta Fulani a jihar Nasarawa kamar yadda sashen Hausa na BBC ya rawaito.

Wasu shuagabannin kungiyarsa ta Kautal Hore kuma makusanta sun tabbatar da batun kama Bodejo a yau Talata.

Sun ce jami’an DSS tare da wasu sojojin Najeriya suka kama shi a garin Lafiya babban birnin jihar Nasarawa.

Sai dai sun ce suna bin bahasi domin ba su san inda aka tafi da shi ba.

A ranar Laraba 17 ga watan Janairu Bello Badejo ya ƙaddamar da rundunar a garin Lafiya inda ya ce za ta taimaka wajen yaƙar ɓarayi da ɓata-gari daga cikin Fulani

Bayanai na cewa jami’an tsaron Najeriya sun kama Bodejo ne kan fargabar cewa kirkiro da ƙungiyar sa-kai zai iya janyo tashin hankali a faɗin ƙasar, kuma kasancewar ba ta da rijista da hukumar farin kaya ta DSS.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories