Ƴan Najeriya Na Buƙatar Bayani Kan Bashin Dala Bilyan 3.3 Na Kamfanin NNPC – Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya caccaki gwamnatin tarayya kan bashin gaggawa na dala biliyan 3.3 na biyan danyen man fetur, Inda ya bayyana cewa yan Nijeriya na bin gwamnati bayani akan batun bashin.

Atiku ya bayyana hakanne a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a birnin tarayya Abuja inda yake cewa kamata yayi gwamnati ta dinga fito da bayanai da al’ummar kasa za su fahimta bawai tayi shiru ba.

Gwamnatin tarayya dai tun a shekarar da ta gabata, 16 ga watan Agusta, 2023, ta samu lamuni ta hannun kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) domin bayadda bashin dala biliyan 3.3

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories