Matasa A Najeriya Sun Bayyana Takaicinsu Kan Rashin Nasarar Aishatu Binani A Kotun Ƙoli

Wasu matasa a jihar Gombe sun bayyana rashin jin dadin game da korar ƙarar da kotun ƙolin Najeriya ta yi wacce tsohuwar ƴar takarar gwamnan jihar Adamawa Aishatu Binani ta shigar inda ta ke ƙalubalantar nasarar Gwamna Ahmadu Fintiri na Jam’iyyar PDP.

WikkiTimes ta tattauna da wani matashi mai suna Zakariyya Abdulkareem mazaunin Gombe kuma dalibi a jami’ar gwamnatin tarayya ta Kashere, inda ya yi zargin cewa kotu ba ta yi Adalci ba kan hukuncin.

Ya ce “abinda kotu tayi ba tayi wa Binani adalci ba, saboda talakawan Yola ita suka zaɓa, ba su zaɓi Fintiri ba. Abin da ya fi tasiri a lamarin Binani shi ne batun addini, saboda sun ce mace ba za ta mulke su ba, kuma Nigeria ƙasa ce wacce ta ke aiki da dokoki (constitution) ba addini ba.”

Zakariyya Abdulkareem ya ce tun da farko an bayyana Aishatu Binani a matsayin wacce ta yi nasara amma sai lamarin ya sauya.

Adamu Ahmad wanda mazauni karamar hukumar Kwami ne ya bayyana cewa da alama kotun ta bi dokokin da ta ga sun dace wajen yanke hukuncin duk da ba haka su ka so ba.

Haka kuma Adamu Ahmad ya ce duk da kasancewar Aishatu Binani matsayin mace ce ba namiji amma kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba ta damar neman kowanne irin mukami na siyasa a dukkanin matakai.

A jiya ne dai kotun ƙolin Najeriya ta yi watsi da ƙarar da ƴar takarar jam’iyyar APC, Sanata Aishatu Binani ta shigar inda ta ke ƙalubalantar nasarar gwamna Fintiri a zaɓen da aka gudanar a watan Maris na 2023.

Halima Lukman

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories