Wani Matashi Ya Angwance Da Ƴan Mata Uku Lokaci Guda A Jihar Benue

Wani matashi mai suna Tersugh Aondona da ke yankin ƙaramar hukumar Kwande jihar Benue ya angonce da mata uku rana daya.

Tun da farko Mista Aondona ya wallafa katin gayyata jama’a zuwa bikin auren ƴan mata da zai angonce da su a shafinsa na Facebook.

A cewarsa, akwai cikakken zaman lafiya, soyayya da hadin kai a tsakaninsa da matansa 3 da kuma daukacin zuri’ar gidajensu.

Tuni dai aka gudanar da shagalin bikin Mista Tersugh Aondona da amarensa da su ka haɗa da Blessing da Nancy da kuma Sulumshima a makarantar Sakandare ta Lante da ke karamar hukumar Kwande a daren jiya Laraba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories