Ya Kamata A Baiwa Ƴan Sandan Najeriya Naira Dubu 250 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi – Masani

Wani masanin harkar tsaro Mathew Ibadin ya bukaci hukumomin Najeriya da su sanya kudin da ya kai naira dubu 250 a matsayin albashi mafi karanci ga jami’an ‘Yan sandan kasar.

Ibadin wanda ya kuma bukaci gwamnati ta amince wajen bada lasisi ga masu bincike dake zaman kansu, kamar yadda ake samu a kasashen da suka ci gaba, yace karin albashin zai kara kaimi ga jami’an dake aiki da rage cin hanci da rashawa da kuma bai wa kwararru a fannoni daban daban damar shiga aikin domin inganta shi.

Masanin harkar tsaron ya kuma bukaci bai wa fitattun mutanen da aka amince da sahihancin su lasisin mallakar bindiga domin kare kan su daga barazanar tsaron da ake fuskanta, ganin yadda ayyukan masu garkuwa da mutane ke dada fadada a cikin kasar.

Daga cikin irin wadannan mutane, jami’in yace akwai sarakunan gargajiya da manyan jami’an gwamnati da malaman makarantu da shugabannin kamfanoni da makamantan su.

Ibadin ya shaidawa Jaridar Daily Trust cewar ya dace gwamnati ta kafa wata hukuma da zata dinga kula da shirin bada lasisin mallakar makaman ga jama’a domin tabbatar da cewar irin wadannan makamai da ake magana basu fada hannun bata gari ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories