Tinubu Ya Jinjinawa Tawagar Super Eagles Kan Nasarar Da Suka Samu A Wasansu Da Angola

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya jinjinawa tawagar ‘yan wasan Super Eagles dake gasar AFCON a Cote d’Ivoire, sakamakon gagarumar nasarar da suka samu a kan kasar Angola, abinda ya basu damar zuwa wasan kusa da na karshe.

Tinubu wanda ya tattauna da ‘yan wasan ta bidiyo daga birnin Paris inda yake ziyara, ya shaida musu cewar miliyoyin ‘yan Najeriya na alfahari da su a kan yadda suke cirewa kasar kitse a wuta dangane da nasarorin da suke samu.

Shugaban ya ce ‘yan Najeriya sun gamsu da irin rawar da suke takawa, saboda haka su na musu fatan alheri wajen ganin sun ci gaba da samun nasara a wasannin da suka rage.

Lokoacin da dan wasan gaba na Super Eagles Victor Osimhen ya zura kwallonsa a ragar Equatorial Guinea, a karawar da suka tashi kunnen doki, 1-1.
Lokoacin da dan wasan gaba na Super Eagles Victor Osimhen ya zura kwallonsa a ragar Equatorial Guinea, a karawar da suka tashi kunnen doki, 1-1. AP – Sunday Alamba
Zaratan ‘yan wasan Super Eagles sun doke Angola da ci 1-0 a karawar da suka yi yammacin jiya, nasarar da ta basu damar zuwa matakin kusa da na karshe na gasar ta AFCON.

Daga cikin wadanda suka aike da irin wannan sakon taya murna da kuma fatar alheri ga kungiyar dake Abidjan, akwai shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio da shugaban majalisar wakilai Tajudeen Abbas da gwamnonin jihohi da kuma masu sha’awar kwallon kafa daga ciki da wajen Najeriya.

A wannan karon ma Ademola Lookman ne ya jefawa Najeriya kwallon ta daya tilo a karawar da tayi da Angolar, yayin da alkalin wasa ya soke kwallon da Victor Osimhen ya jefa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories