Sarkin Daura Alhaji Umar Farouk ya ziyarci tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ziyara ta musamman a gidansa da ke Daura a jihar Katsina a arewacin Najeriya.
Buhari Sallau wanda shi ne tsohon mataimaki ga Muhammad Buharin ya wallafa hotunan ziyarar a shafinsa na Facebook.
Masarautar ta Daura ita ce mahaifar tsohon Shugaba Buhari.