Ku Nemi Makami Ku Kare Kan Ku-Dikko Raɗɗa

Gwamna Dikko Raɗɗa na jihar Katsina ya shaida wa mazauna jihar da kar su yi ƙasa a gwiwa wurin ɗaukar matakin kare kansu daga hare-haren ƴan bindiga.

 Ya ce maimakon su rika dogaro da kariyar gwamnati a koda yaushe, kawai su kafa ƙungiyoyin kare kai.

Gwamnan ya yi wannan kiran ne a ranar Juma’a a gidan gwamnati da ke garin Katsina yayin gudanar wani gagarumin taron gaggawa akan tsaro.

Taron ya samu halartar sarkin Katsina da na Daura, Dr Abdulmumini Kabir Usman da Dr Umar Farouq Umar ,ƴan kasuwa da kuma shugabannin tsaro a jihar.

“Dole ne mu sake tsari game da yanayin tsaro a jihar, sannan kuma dole ne mu ɗauki matakin nemo mafita, don magance waɗannan matsaloli.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories