EFCC Na Neman Matar Emefiele Da Wasu Mutum Uku Ruwa-A-Jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC) ta bayyana cewa tana neman Margaret Dumbiri Emefiele, wacce ita ce matar tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.

Haka kuma hukumar ta bayyana cewa, tana neman wani Eric Ocheme Odoh (namiji) da Jonathan Omoile (namiji) da kuma Anita Joy Omoile (mace) bisa tuhumar haɗa baki da tsohon gwamnan babban bankin ƙasar, wajen satar wasu maƙudan kuɗaɗe mallakin gwamnatin tarayya.

Hukumar ta EFCC, a cikin sanarwar da ta fitar ta kuma tuhumi wadanda ake nema da aikata laifukan da suka haɗa da samun kudi ta hanyar ƙarya da sata, wanda ya sabawa sashe na 411, 287 da 314 na dokar laifuka ta jihar Legas.”

Ta nemi masu bayanin inda waɗanda ake nema suke, da su tuntuɓi kowane ofishinta a Najeriya, ko su kira 08093322644.

A halin yanzu dai tsohon gwamnan na babban bankin na fuskantar shari’a kan tuhume-tuhume 20 da suka hada da bayar da cin hanci da rashawa, haɗa baki da cin amana da satar kuɗaɗen da suka kai dalar Amurka fiye da miliyan shida ($6,230,000.00).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories