Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutum 9, Sun Yi Garkuwa Da Tsohon Daraktan CBN A Kaduna

Wasu Ƴan Bindiga sun harbe mutum tara a yankin Kwasam da ke ƙaramar hukumar Kauru da kuma unguwar Gwada da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna.

 Sannan kuma Ƴan bindigar sun yi awon gaba da wasu mutane 35 da suka haɗa da Babban Daraktan Bankin Najeriya (CBN) mai ritaya mai suna Zakariya Markus, tare da ɗan uwansa da matar sa.

Haka kuma ƴan bindigar sun jikkata mutane tara a wannan harin da suka kai.

 Sannan kuma an kashe mutane shida, an sace biyar, biyu kuma sun jikkata a ƙaramar hukumar Kauru yayin da aka kashe mutane uku, sannan aka sake jikkata bakwai,tare da yin garkuwa da mutane 30 a ƙaramar hukumar Igabi ta jihar.

Rahotanni sun bayyana cewa, lamarin ya faru ne a ranar Juma’a da misalin karfe 10 na dare inda ƴan bindigar suka yi wa yankin dirar mikiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories