A Bar Wanda Ba Musulmi Ba, Ya Shiga Makka Da Madina?

Cikin abubuwan farko da Annabi ya gabatar bayan zuwansa Madina shi ne wannan yarjejeniya:

“Da Sunan Allah mai rahama mai jin ƙai, wannan yarjejiniya ce daga Muhammadu manzon Allah, tsakanin musulmi masu Imani daga Ƙuraishawa da mutanen Madina da duk wadanda su ke tare da su (Ahlul Kitabi), su ka sha wahala tare da su, wadannan Al’umma ɗaya ne babu bambanci a tsakaninsu. Musulmai yan uwan juna ne, haka kuma Yahudu (Ahlul Kitab) wadanda su ke tare da mu sun cancanci taimako da daidaito yadda ba za’a cutar da su ba, kuma ba za’a goyawa maƙiyinsu baya ba. Kwanciyar hankalin musulmi ta su ce gaba ɗaya don haka babu wata yarjejeniya daga wani ɓangare sai dai a dunƙule, dole a tsayar da adalci bai ɗaya a kan kowa da kowa (Musulmi da Ahlul Kitabi)” (kaɗan daga cikin doguwar yarjejeniyar ke nan)

Lokacin wannan yarjejeniya akwai kabilun Yahudawa uku manyan a Madina: Banu Ƙainuƙa, Banu Ƙuraiza da Banu Nadir. Banu Ƙainuƙa su ne waɗanda Annabi ya fara kora sakamakon karya yarjejeniyarsu bayan an yi yaƙin Badar. Amma ragowar sun ci gaba da zamansu karkashin yarjejeniyar. Bayan yakin Badar, sai Ka’ab Bn Sharaf, shugaban Yahudawan Banu Nadir ya sulale zuwa Makka domin kulla yarjejeniya da su a zo a yaki Annabi. Allah ya tona asirin Ka’ab kuma sakamakon karya Yarjejeniya wadda ta ce “Ba za’a baiwa Ƙuraishawa da abokansu mafaka ba.” Don haka annabi ya ce hukuncin cin amanar yarjejniya kisa ne (kamar yadda a kowacce shari’a treason hukuncin kisa ne). Bayan Kashe Ka’ab, Yahudawan Banu Nadir sun zauna cikin tsoro, amma kuma sai kiyayyarsu ga annabi ta ƙaru don haka sai su ka shirya kashe Annabi ta hanyar yaudararsa da ya zo yin muƙabala da su a cikin unguwarsu da ke arewacin Madina. Annabi ya shirya zuwa amma sai wani dan kabilar Banu Nadir wanda ya musulunta ya kawo masa labarin shirin kashe Annabi da su ke yi, don haka sai ya ki zuwa. Wannan cin amana da su ka yi tare da karya yarjejeniyar kundin tsarin mulkin Madina wanda su ka sakawa hannu ya sa Annabi ya umarci a kewaye unguwar tasu. Bayan tsawon makonni biyu, sun mika wuya inda Annabi ya umarce su da ficewa daga madina.

Bayan Ƙuraishawa sun yi nasara a kan musulmi a yakin Uhud, ‘yan Banu Nadir sun kulla kawance da Quraishawa inda su ka zuga su a kan cewa su fito kwai-da-kwarkwata domin murkushe Annabi da Musulmi gaba daya a Madina. Wasu kabilun larabawa irinsu Banu Ghatafan, Sulaym da Asad su ka shiga cikin wannan qawance inda su ka tara sojoji sama da 10,000 su ka nufi Madina. Ganin cewa sojojin Annabi a lokacin da ya sami wannan labari ba su wuce 3000 ba, sai ya sa aka fara gina wani rami a arewacin Madina. Wannan rami shi ya sa dakarun hadin gwiwa su ka kasa far wa Madina amma sun zauna a bakin wannan rami tsawon kusan makonni uku. Su kuma kabilar Yahudawa ta karshe da ke zaune cikin Madina, wato Banu Qurayza, sai su ka fara tattaunawar sirri da sojojin kawance ganin cewa kamar za’a murkushe Annabi da musulmi, domin su kuma unguwarsu na kudancin Madina. A karshe dai sakamakon hadarin hamada wanda ya zo ya yi kaca-kaca da tantunan sojojin haɗin-gwiwa, da rashin abinci da ruwa ya tilasta musu watsi da shirin na su su ka koma Makka. Shi kuma Annabi bayan wannan nasara daga ubangiji sai ya sa aka kewaye unguwar Banu Quraiza wanda aka yi kusan makonni kafin su mika wuya. Kasancewar sun ci amanar yarjejeniyarsu da Annabi, musamman a lokacin yaki, ya sa an kama mazajensu wadanda aka yiwa hukuncin kisa kuma aka kori mata da yara daga garin.

Tsarin da Annabi ya gina a Madina shine na zama tare da Ahlul Kitab cikin amanar yarjejeniya, kuma bai hana su yin addininsu da mu’amalarsu su ba matukar sun kare yarjejeniya.

Sannan mun ga yadda ya karbi bakuncin Kiristoci kimanin 60 da suka zo daga daga garin Najran, Annabi ya sauke su a masallacin sa mai alfarma, su ka yi mukabala tare, sannan ya ba su dama su ka yi sallarsu a cikin masallacinsa, duk da cewa “Trinatarians” ne, wato masu Allah uku, ainihin maudu’in da a kansa su ka yi makabala.

Muna sane kuma da hukuncin Allah cikin suratul Tauba, inda Allah ya umarce mu da cewa ko ana cikin yaki, ba Ahlul Kitabi ba, hatta mushrikai

Q9:6 “Idan wani daga mushirikai ya nemi maƙwabtakarka to, ka ba shi maƙwabtakar har ya ji, maganar Allah, sa’an nan ka isar da shi ga wurin amincewarsa. Wancan fa domin lalle ne su, mutãne ne waɗanda ba su sani ba”

Idan mushriki bai shiga cikin mutanensa ya yake ku ba, ya kuma nemi mafaka a wajenku, to wajibi a bashi mafaka har iya zamansa, idan kuma zai tafi to a yi masa rakiya tare da kariya.

Har Annabi ya yi wafati akwai Ahlul Kitab a madina kuma bai hana su shigowa garin ba. Amma daga baya bayan musulmi sun mamaye Arabia sai su ka kirkiro wannan doka ta hana wadanda ba musulmi ba shiga garuruwan Makka da Madina. Wannan doka, doka ce ta larabawa kawai, ba dokar Allah ko Annabi ba ce.

Ali Abubakar Sadiq ya rubuto daga Kano

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories