Lokacin Azumi: Ɗaukar Nauyin Karatu Ko Ciyar Da Bayin Allah?

A ‘yan shekarun nan kusan duk lokacin da watan azumi ya ƙarato sai muhawara ta taso akan me ya fi dacewa masu kuɗi su fifita tsakanin ɗaukar nauyin karatun manyan malamai a kafofin yaɗa labarai ko ciyar da talakawa waɗanda ba su da abinda za su ci.

Wannan ya biyo bayan halin ƙunci da talauci da ya addabi al’umma a waɗannan shekarun wanda a bana al’amarin ya ƙara ta’azzara saboda abinci ya yi tsadar da bai taɓa yin irinta ba kuma talakawa ba su da kuɗin saye. Akwai tsoron cewa gidaje da yawa za su kai azumi ba tare da samun abin buɗa baki ba.

Masu goyon bayan sayen fili don sanya karatu musamman manyan malamai waɗanda su ne aka fi sa karatunsu su na kafa hujja da cewa ciyar da ruhi ya fi ciyar da gangar jiki. Ko a bara na ji yadda wani daga cikinsu ya ɗau zafi sosai akan wannan mas’alar. Masu ra’ayin a fifita ciyarwa su na kallon irin mummunan halin ƙunci da fatara da ake ciki ne wajen kafa hujja.

Na yi nazari akan hujjojin ɓangarorin guda biyu kuma wannan shi ne ra’ayina:

1- Idan zai yi wu a haɗa guda biyun zai fi amma idan ɗaya kawai za a yi to ni ina ganin a ciyar da bayin Allah

2- Ban yarda da cewa dole sai an ɗauki nauyin sa karatun malamai a radio kawai ne za a raya zuciyar mutane ba domin akwai malamai a kowanne lungu da saƙo da mutum zai iya zuwa ya ji karatunsu. Ba wani malami shi kaɗai da za a ce dole sai an ji karatunsa ruhi zai rayu komai ilminsa

3- A wannan lokaci da mu ke ciki akwai alternative hanyoyi na yaɗa karatukan malamai a social media kamar WhatsApp da Facebook da sauransu waɗanda mai son jin karatun kowanne malamai zai iya amfani da su. Ni ma ta WhatsApp na ke jin tafsirin malamai duk shekara ba ta radio ba. Ban san alternative maganin yunwa ba!

4 – Har yanzu babu wani bincike na ilmi (audience analysis) da aka gabatar akan tasirin wannan yawan sa karatuka da ake yi. Da za a yi bincike wataƙila a gano ba lallai ne hakan ya na da tasirin da muke zata ba. Saboda zuwan wayoyin hannu, kaɗan ne daga cikin mutane masu yawo da radio. Wanda ya ke da waya kuma ya na son jin karatu, social media zai fi masa sauƙi. Da ma rashin wuta tun tuni ya ragewa mutane da yawa kallon talabijin

5- Da muna yara gidan radio ɗaya ne tak – FRCN Kaduna – su ke sa karatun Sheikh Abubakar Gumi (Rahimahullah) kuma DUK Nigeria ya wadatar. A nan Kano kuma Radio Kano da CTV/ARTV ne kawai su ke sa karatun Sheikh Isa Waziri (Rahimahullah) da daddare amma a haka mu ke jira mu saurara mu da iyayenmu. Me ya sa yanzu ake buƙatar tashoshi ba adadi? Idan yawan sa karatu a radio ne ya ke gyara mutane, ya akai mutanen wancan lokacin su ka fi na yanzu kirki da nagarta?

6 – Duk shekara ina jin yadda ake zuwa da dogon list ana karantawa na tashoshin da su ke sa karatukan malamai a garuruwa daban-daban da lokutansu. Anya elitism bai shiga harkar ba ta yadda za a dinga amfani da hakan wajen nuna karɓuwa da ƙarfin tasiri? Iya yawan tashoshin da su ke sa karatun malami iya muhimmancinsa! Anya wannan ba buɗewa Shaiɗan kofa ba ne?

Duba da wannan na ke ba da shawarar cewa a bana dai a yi haƙuri da yawan ɗaukar nauyin sanya karatun malamai a kafofin yaɗa labarai. A wadatu da abinda tashoshin gwamnati za su yi na sadaka. A yi amfani da kowacce Naira wajen tallafawa talakawa da abinci. Kamar yadda malami ba zai iya karatu ba idan bai ci ba, shi ma talaka ba zai iya saurara ba idan ya na rigima da cikinsa.

A sai abinci a bawa talakawa kowa ya ci ya ƙoshi ya ɗau Al-qur’ani da shimfida ya je ya saurari tafsiri a masallacin unguwarsu. Wannan ya fi lada a gurin Allah kuma ya fi raya ruhin mutum! Mai son jin karatun wani shahararren malami a tura masa ta WhatsApp.

Allah ya sa mu dace kuma ya karɓi ibadunmu!

Dr. Ibrahim Siraj Adhama

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories