Kalaman Gwamna Abba Kabir Yusuf Kan Hukumar Hisbah: Gyara Ko Buɗe Ƙofar Ɓarna?

Maganar gaskiya ban ji daɗin kalaman da gwamna Abba K. Yusuf ya yi a lokacin da Hisbah suka kai masa ziyara bayan dawowarsa daga tafiya ba. Kamar daman abin da yake ransa ke nan tun kafin ya dawo? Ko abin ɓoye ne ya fito fili, tunda an yi zargin cewa ku kuka bayar da umarni a saki waccar uwar tambaɗaɗɗun bayan Hisbar ta yi aiki a kanta?

Gwamna ka nuna damuwa kan yadda ake kama masu baɗala maza da mata ana jefa su a mota tamkar dabbobi, amma bamu taɓa jin ka nuna damuwa kan yadda waɗannan tambaɗaɗɗu ke yaɗa ɓarna irin ta rayuwar dabbobin cikin jama’armu ba. Wasu lokutan a ƙoƙarin gyara fa dole sai an tsoma hannuwa cikin datti, kuma Bahaushe ma na cewa gyaran Masai sai an shiga daga ciki.

Wanne irin kamu kake so a yiwa waɗannan iyayen baɗalar idan ba irin wanda Hisbar ta ke yi musu ba? Abin da suke yi ai daman rayuwar dabbobin ce, idan ka so za ka iya kiran rayuwarsu irin ta Karnuka, tunda kullum babu abin da suke yi sai yaɗa ɓarnar neman maza da neman mata ga junansu. Shi kenan sai a zuba musu idanu ko binsu ta laluma, bayan ba shi ne yaren da suka fi ganewa ba???

Gwamna ka yi kuskure wajen fayyace wannan lafazin naka a bainar jama’a, domin babu abin da zai janyo sai rugujewar kimar hukumar Hisba, kuma ya janyo masu yaɗa ɓarnar su ji a ransu cewa gwamnatinsu ce. Idan ma hakan gyara ne ai kamata ya yi ka bari sai ka kulle ƙofa sannan ka gaya musu gyaran da za su yi wajen gudanar da ayyukansu. Muna kira da ka sake fitowa ka gyara kuskurenka, domin wannan kaɗai ya isa hujja ga shugaban hukumar ya yi murabus idan ya san ciwon kansa.

Ibrahim Ishaq Danuwa Rano ya rubuto daga Kano – Najeriya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories