Ƴan Bindiga A Jihar Kaduna Sun Yi Awon Gaba Da Mutane Fiye Da 61

Aƙalla mutum 61 ƴan bindiga suka sace a wani ƙauye da ke Jihar Kaduna a Nijeriya, kwanaki kaɗan bayan sace ɗalibai kusan 300 daga wata makarantar firamare, kamar yadda mazauna garin suka faɗa a ranar Talata.

Shaidu sun ce ƴan bindigan sun kai hari ne ƙauyen Buda da tsakar daren Litinin, inda suka buɗe wuta, wani salo na tsorata mutane.

Ba a samu jin ta bakin kwamishinan tsaro da ƴan sanda ba kan wannan lamari zuwa lokacin wallafa wannan labarin.

Ƙauyen Buda na da nisan kilomita 160 daga Garin Kuriga, inda aka sace ɗaliban firamare a makon da ya wuce.

Wani ɗan garin Lawal Abdullahi ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa ba ya nan ƴan bindigan suka dira, amma matarsa na cikin waɗanda aka sace.

“Matata na cikin mutum 61 da ƴan bindigan suka sace. Har yanzu muna jiransu su kira mu a kan batun kudin fansa,” Abdullahi ya shaida wa Reuters ta wayar tarho.

“Muna fama da hare-hare tsawon lokaci. Lamarin na ƙara taɓarɓarewa, yana tursasa mazauna da manoma a ƙauyuka suna tserewa zuwa wuraren da babu fargaba,” wani mazaunin garin Danjuma ya faɗa.

An shafe shekaru ƴan bindiga na cin karensu babu babbaka a arewacin Nijeriya, inda suke kai hari kan ƙauyuka da tare ababen hawa a kan manyan tituna da kuma makarantu, duk don satar mutane don neman kuɗin fansa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories