Sojoji Sun Ceto Wasu Mata 5 Da Jarirai Da Aka Sace A Zamfara

Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Operation Hadarin Daji, OPHD, sun yi nasarar ceto wasu mata biyar da jarirai biyu bayan shafe watanni biyu a hannun ƴan bindiga a jihar Zamfara.

 Rahoton na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na rundunar, Laftanar Suleiman Omale ya fitar a garin Gusau ranar Alhamis.

 “Cikin jajircewa da ƙwarewa dakarun mu sun yi nasarar kutsawa dajin Kuyambana na jihar Zamfara inda suka yi nasarar ceto mata biyar da jarirai biyu.”

“An sace waɗannan mata ne a watan Janairun 2024 daga ƙauyen Marange da ke ƙaramar hukumar Kagara a jihar Neja.

 “Waɗanda aka sacen sun shaƙi ƴanci ne bayan shafe watanni a hannun ƴan bindigan.Nasarar ceto su ya biyo bayan Buɗe wuta da ƴan Banga suke yi a garin na kuyambana.

Laftanar Suleman ya ƙara da cewa waɗanda aka ƙwato yanzu haka an miƙa su ga hukuma don ganin an sada su da iyalan su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories