Abba Gida-Gida Ya Yi Kakkausar Jan Kunne Ga Masu Dafa Abincin Azumi

A wata ziyarar gani da ido da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya kai gidan maza dake ciki garin Kano domin ganin yadda shirin ciyarwa azumi ke gudana gwamnan ya nuna ɓaci ransa matuka.

A faifan bidiyo da ya bayyana an dai ga gwamnan ya tsare masu dafa abincin yana tuhumar su cikin ɓaci rai sakamakon ganin irin ƙasƙantaccen abincin da suke dafawa .

Gwamnan dai ya yi kakkausar jan kunne game da wannan lamari inda ya shaida cewa baya so ya sake dawowa ya ga an maimaita irin hakan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories