Gwamnan Nasarawa, A.A Sule Ya Ziyarci Tsohon Shugaban Najeriya Buhari

Gwamnan jihar Nasarawa Engr. Abdullahi A. Sule ya ziyarci tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a garin Daura da ke jihar Katsina.

Tun da farko tsohon mataimaki na musamman ga tsohon shugaban, Buhari Sallau ne ya wallafa hotunan ziyarar a shafinsa na Facebook a yau Asabar kamar yadda WikkiTimes ta gani.

A cikin tawagar da su ka kaiwa tsohon shugaban ziyarar akwai tsohon Gwamna jihar ta Nasarawa kuma tsohin shugaban jam’iyyar APC na kasa Sen. Abdullahi Adamu, da Sarkin Lafiya, HRH. Mai shari’a Sidi Bage Muhammad I, da kuma mai girma Atoni-Janar kuma kwamishinan shari’a na jihar Nasarawa, Barr. Labaran Magaji.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories