Jami’an DSS Sun Kama Aisha Galadima,Jigo A Gwamnatin El-Rufa’i

Hukumar tsaron farin kaya (DSS) sun kama Aisha Galadima, daya daga cikin ƴar gwagwarmayar siyasar tsohon gwamnan Nasiru El-Rufa’i.

 Rahotanni sun bayyana cewa Kamen na ta ya faru ne biyo bayan wani rubutu da ta wallafa a shafinta na Facebook, inda ta fito ta soki Gwamna Uba Sani.

 An sami rahoton cewa Jami’ai ne suka yi wa Aisha Ɗaukar amarya a yau Lahadi a gidanta da ke Kaduna.Kamen nata ya bayyana ne ta bakin wani Ɗan uwanta

“Yanzun nan jami’an DSS Su ka dira Gidan Aisha da ke Tudun Wada Kaduna inda suka tafi da ita ,”

Idan dai ba a manta ba a kwanakin baya an ji Gwamna Uba Sani ya fito ya bayyana irin dimbin basukan da tsohuwar Gwamnatin El-Rufa’i ta bari wanda har hakan ya jawo cece-kuce tsakanin sa da tsohuwar Gwamnati

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories