Wani Harin Jirgin Sama Ya Yi Nasarar Murƙushe Ƴan Ta’adda A Maiduguri

Rundunar sojin sama ta Operation Hadarin Kai (OPHK) ta kai wani hari a maɓoyar ƴan ta’addan ISWAP, inda suka yi nasarar kashe ƴan ta’adda sama da 30 a kauyen Koleram da ke gabar tafkin Chadi.

 A cikin wata sanarwa da Daraktan hulɗa da jama’a da yada labarai na rundunar sojojin ya fitar a ranar Talata a Abuja, AVM Edward Gabkwet, inda ya Ke cewa harin da aka kai ta sama a ranar 13 ga watan Afrilu wani gagarumin nasara ne ga ayyukan ta’addanci da ya Addabi yankin Arewa maso Gabas.

 Ya ƙara da cewa harin wata gagarumar nasara ce inda aka yi rugurugu da ƴan tanada kimanin su 30.

Haka kuma Gabkwet ya zayyano sunayen manyan kwamandojin ƴan ta’addan da aka murƙushe waɗanda suka hada da Ali Dawud, Bakura Fallujah, da kuma Malam Ari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories