Ziyarar Amurka: Kashim Shettima ya dawo Najeriya bayan samun matsalar jirgi

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya katse tafiyarsa zuwa kasar Amurka tare da dawowa Najeriya.

Sanarwar data gabata ta bayyana cewa Shettima ya bar Najeriya zuwa kasar Amurka domin halartar wani taron bunkasa kasuwancin kasashen Africa Wanda za a yi a birnin Dallas dake jihar Texas.

Sai dai, da yammacin ranar Litinin din nan ne Stanley Nkwocha, mai taimakawa Shettima a bangaren sadarwa da yada labarai ya bayyana cewa Shettima ba zai samu damar halartar taron ba.

A cewar Nkwocha, ministan harkokin kasashen waje, Yusuf Maitama Tuggar, shine yanzu zai wakilci shugaba Bola Tinubu a wurin taron.

Nkwocha ya sanar da cewa Shettima ya dawo gida Najeriya bisa shawarar kwararru bayan jirginsa ya samu tangarda wacce bai bayyana yanayinta ba.

Kazalika, ya kara da cewa Shettima ya dawo Najeriya kuma zai cigaba da gudanar da harkokin gwamnati da mulki.

KARANTA: Dalla-dalla: NLC ta fayyace dalilin kayyade N615,000 a matsayin mafi karancin albashi

Hadimin na Shettima ya bayyana cewa taron da za a yi a Amurka zai samu halartar shugabannin kasashen Afrika da dama da suka hada dana Liberia, Malawi, Angola, Botswana, Lesotho da Cale Verde.

A yammacin ranar Litinin din ne dai Atiku Abubakar ya soki lamirin gwamnatin tarayya saboda shugaba Tinubu da Shettima sun fice sun bar kasa a yayin da ya kamata su zauna domin aiki tukuru wajen nemawa jama’a mafita.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories