Bashin $350m: Majalisar Jihar Kaduna ta fara binciken El-Rufai

Kwamitin da majalisar dokokin Jihar Kaduna ta kafa ya fara sauraron jin yadda gwamnatin da ta gabata ta sarrafa kudaden jihar a tsawon shekaru takwas da suka gabata.

Binciken kwamitin majalisar zai fi mayar da hankali ne akan bin ba’asi da kididdigar yadda gwamnatin ta sarrafa Dalar Amurka miliyan dari uku da hamsin ($350) data ranto daga ketare.

Malam Nasir El-Rufai ne ya jagoranci gwamnatin jihar Kaduna daga 2015 zuwa 2023 kuma gwamnatinsa ce ta ciyo bashin da ake magana.

Shugaban kwamitin, Magaji Henry, ya ce sun fara wannan aikin ne domin sanin yadda jihar ta tsinci kanta dumu-dumu a cikin dumbin bashi daga watan Mayu na shekarar 2015 zuwa watan Mayu na shekarar 2023.

Kwamitin na wucin gadi yana da jimillar mambobi 13.

A yayin zaman kwamitin na yau, Talata, wanda shine zama na farko, an saurari biyar daga cikin shaidu 16 da kwamitin zai saurara.

A cewar Henry, za a kira sauran shaidun a yayin da binciken kwamitin ya kara nisawa.

KARANTA: Zamu zakulo tare da kakkabe ma’aikata da aka dauka aiki da takardun bogi – FG

Kwamitin ya bayyana cewa aikinsa shine ya gano gaskiya da tabbatar da cewa an samu tsafta a bangaren kashe kudaden gwamnatin jihar.

Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya sha korafin cewa jihar Kaduna bata da isassun kudin da zata gudanar da mulki saboda bashin da ake bin jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories