EFCC:Ma’aikacin Kotu Ya Shiga Tasku Bayan Sama Da Faɗi Da Naira Miliyan 3.8

EFCC ta Yi Nasarar cafke wani ma’aikacin kotu sakamakon zargin sa da ake yi da laifin yashe kuɗin wani marigayi ta hanyar amfani da sa hannu na ƙarya.

A cewar EFCC ta bayyana cewa aikata wannan laifi ya karya sashe na 311 na Penal Code CAP 89 Laws of Northern Nigeria 1963, da kuma hukunci a karkashin sashe na 312 na wannan dokar.

Mai laifin mai suna Dandare ana tuhumar sa ne da laifuka biyu wanda suka haɗa da karkatar da kudi N3.8m mallakar wani marigayi dan kasuwa mai suna Alhaji Ladan da kuma satar fasahar sa hannun magajin mamacin na ƙarya 

 A karar da hukumar EFCC ta shigar mai lamba ZMJ/GS/13C/2024, ana zargin Dandare ne da karkatar da kudi naira miliyan N3,837,634.46, wanda ma’aikatar kudi ta jihar Zamfara ta biya ga iyalan marigayi Alhaji Ladan Mada a ranar 4 ga watan Disamba 2012, a lokacin yana rike da mukamin magatakardar Kotun Shari’a ta 1, Samara Gusau, Jihar Zamfara.

 EFCC ta Ce wanda ake zargin laifin da ya aikata cin amana ne da ya saɓawa sashe 311 na kundin laifuffuka na CAP 89 na Arewacin Najeriya na 1963, kuma hukuncin da ke ƙarkashin sashe na 312 na wannan doka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories