Kano: Abba ya rattaba hannu kan sabuwar dokar ‘gwaji dole’ kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya rattaba hannu kan sabuwar dokar ‘gwajin lafiya dole’ kafin daura aure.

A ranar Talata ne Abba ya saka hannu akan dokar bayan ta samu amincewar ‘yan majalisar dokokin jihar Kano.

A wani takaitaccen Sako da Abba ya wallafa a shafinsa na ‘X’ ya bayyana cewa an yi dokar ne domin rage samun afkuwar matsalolin lafiya da kan iya shafar ma’aurata ko ‘ya’yan da zasu haifa.

Abba Kabir

Daga cikin gwaje-gwajen da dokar ta kayyade akwai gwajin nan na kwayoyin halitta (genotype), ciwon hanta (Hepatitis), da Kanjamau.

Saka hannu akan sabuwar dokar na nufin cewa babu wani aure da za a daura ba tare da masu niyyar aure sun gabatar da takardar shaidar gwaji daga asibitin gwamnati ba.

KARANTA: Sarkin Kano Ya Jajanta wa Shekarau Kan Ɓarnar Da Gobara Ta Yi Masa

Kazalika, dokar ta haramta nuna kyama ko muzgunawa masu dauke da cutar kanjamau, ciwon hanta, ko Kuma wata larura.

A karshe, Abba ya yabawa mambobin majalisar dokokin jihar Kano bisa kirkirar dokar.

Kirkirar wannan doka ya saka Kano cikin sahun jihohin Jigawa da Bauchi wadanda tuni gwamnatocinsu suka kaddamar da irin wannan doka a baya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories