Badakalar N2.7b: EFCC zata gurfanar da tsohon minista Hadi Sirika tare da diyarsa

Hukumar yaki da cin hanci da yiwa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) ta sanar da cewa zata gurfanar da tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, tare da wasu mutane uku.

EFCC ta ce zata gurfanar da Sirika tare da sauran mutanen uku ciki harda diyarsa, Fatima, bisa zargin cin zarafin ofishin minista da kuma badakalar kudi da yawansu ya kai biliyan biyu da miliyan dari bakwai.

A cewar EFCC, za a gurfanar da Sirika, minista a gwamnatin tsohon shugaba Buhari, a gaban Mai shari’a, Sylvanus Oriji, na babbar kotu dake unguwar Maitama a Abuja.

Sirika tare da diyarsa, Fatima, da Jalal Hamma da Al-Duraq Investment Ltd na fuskantar tuhuma guda shida da suka shafi harkallar kwangiloli.

A ranar 23 ga watan Afrilu ne EFCC ta tsare Sirika a Abuja bayan hukumar ta fara bincike akan badakalolin da ake zarginsa da aikatawa lokacin tsohuwar gwamnatin Buhari.

DUBA WANNAN: Dalla-dalla: NLC ta fayyace dalilin kayyade N615,000 a matsayin mafi karancin albashi

EFCC ta tsare tsohon minista Sirika bayan ya amsa gayyatar hukumar domin amsa tambayoyi akan zarge-zargen da ake yi masa.

Da fari dai anso gurfanar da Sirika a gaban kotu tun ranar Talata Amma sai EFCC ta roki a kara mata lokaci domin sake gyara a tuhume-tuhumen da ake yi masa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories