Guguwa Ta Yi Ajalin Yarinya,Mutum 15 Sun Raunata A Gombe

Nannauyan guguwa ta yi Ajalin wata yarinya tare da jikkata mutane 15 da kuma lalata dukiyoyi na miliyoyin Naira a Yankin Wuro Hampate, Maitama, Nayi Nawa da kuma Bagadaza duk a cikin garin Gombe.

Jaridar City & Crime ta tattaro cewa lamarin dai ya faru ne a ranar Litinin da misalin karfe 5 na yamma a lokacin da garin ya sami saukar ruwan sama na farko wanda hakan yayi sanadiyyar lalacewar sama da gidaje 100 .

Wani mazaunin unguwar Bagadaza, Malam Abba Muhammad, ya ce rufin kwanon gidan sa mai daki biyu duka sun yaye, yayin da katangar gidan kuma ta ruguje, faruwar lamarin ya tilastawa iyalansa fakewa gidan makwabta.

Shugaban Unguwar Wuro Hampate, Malam Isa Adamu, ya ce lamarin ya sa iyalai da dama suka rasa matsugunin su .

 Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar (SEMA) ta ziyarci yankunan da abin ya shafa domin tantance irin asarar da aka don sanin irin tallafin da za a yi musu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories