‘Annabawa ma sun je’: Hadi Sirika ya rarrashi ‘Yarsa a zauren kotu

A yau, Alhamis, ne hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, tare da ‘yarsa, Fatima, da kuma surukinsa a gaban kotu.

Babbar kotun Abuja ta amince da bayar da belin Sirika tare da sauran wadanda aka gurfanar tare da shi akan N100m kowanne mutum tare da mutum biyu da zasu tsayawa kowa.

A cewar kotun, dole wadanda zasu tsaya domin karbar beli su kasance ‘yan kasa nagari kuma masu kadara a Abuja.

Alkaline kotun, Jastis Sylvanus Oriji, ya bada umarnin a tsare wadanda aka gurfanar a gidan yari idan basu cika sharadin beli ba.

A wani faifan bidiyo Dake yawo a dandalin sada zumunta an ji Sirika yana kokarin rarrashin diyarsa, Fatima, tare da fada mata cewa ‘annabawa ma sun je’.

”Ya isa, Fatima, ya isa, ki saki jiki mana, annabawa ma sun je ko. Ba sun gama nasu ba, su tsaya su ga abinda Allah zai yi, ” kamar yadda Sirika ya furta.

KARANTA: Zamu zakulo tare da kakkabe ma’aikata da aka dauka aiki da takardun bogi – FG

Sirika tare da diyarsa, Fatima, da Jalal Hamma da Al-Duraq Investment Ltd na fuskantar tuhuma guda shida da suka shafi harkallar kwangiloli.

A ranar 23 ga watan Afrilu ne EFCC ta tsare Sirika a Abuja bayan hukumar ta fara bincike akan badakalolin da ake zarginsa da aikatawa lokacin tsohuwar gwamnatin Buhari.

EFCC ta tsare tsohon minista Sirika bayan ya amsa gayyatar hukumar domin amsa tambayoyi akan zarge-zargen da ake yi masa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories