Hadi Sirika, Ɗiyarsa, Za Su Gurfana Gaban Kotu Bisa Badakalar N2.7bn

Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon kasa, EFCC, za ta gurfanar da tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, a gaban mai shari’a Sylvanus Oriji na babbar kotun taraya da ke Abuja a yau Alhamis.

 Hadi Sirika,zai gurfana gaban kuliya ne bisa tuhume-tuhume shida da ake yi masa.

 Za a gurfanar da shi ne tare da wasu mutane uku da suka haɗa da ƴarsa Fatima;  Jalal Hamma da Al-Duraq Investment Ltd, bisa laifin yin sama da faɗin da kimanin Naira biliyan 2.7.

A cigaba da binciken da EFCC ke yi kan badakalar kuɗaɗen da ake zargin tsohon ministan ya yi, “ciki har da kwangilolin da ma’aikatar sa ta baiwa ɗiyar sa da kuma sirikin sa karkashin mulkin sa,A yanzu dai Hukumar ta yi nasarar tsare shi tun a ranar 23 ga Afrilu a Abuja’’.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories